14 Janairu 2020 - 19:52
Iran Ta Gargadi Kasashen Turai Akan Matakin Da Suka Dauka

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar, ta gargadi kasashen turan da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita, akan abunda zai iya biyon bayan matakin da suka dauka yau Talata, na tilastawa Iran yin aiki da yarjejeniyar da aka cimma da ita, bisa da’awarsu ta cewa Iran din ta sabawa yarjejeniyar.

ABNA24- ta rawaito Ministan harkokin wajen kasar  Iran, Muhamad Jawwad Zarif, ya ce, lalle idan kasashen turan suka kama hanyar zama ‘yan amshen shatan Amurka, to kuwa dole su rungumi abunda zai biyo baya.

Mista Zarif, ya kara da cewa wannan ba shi da wata alaka da cewar kasashen turan, wata hanya ce ta kare yarjejeniyar ta 2015 daga durkushewa.

Matakin da kasashen turan uku Biritaniya, Jamus, da kuma Faransa suka sanar a yau, na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya bukace su yi watsi da yarjejeniyar.

Jamhuriya musulinci ta Iran, ta ce a shirye ta sake nanata cewar za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar ta kasa da kasa mai cike da mahimmanci, amma kuma tana shaidawa duniya cewa a shirye ta ke ta maida martani mai karfi kan duk wata anniya ta kasashen turan akan wata muguwar anniyarsu kan yarjejeniyar.